Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Wadannan hare-hare sun hada da laifukan ta’addanci kai tsaye kan fararen hula, tada bama-bamai da kuma tsare wasu fararen hula, lamarin da ke nuni da cewa 'yan mamaya na ci gaba da kai farmaki duk da sanarwar tsagaita bude wuta.
Karya yarejejeniyar tsagaita bude wuta da aka samu a dukkan sassan Zirin Gaza na nuni da cewa 'yan mamaya ba su da niyyar kawo karshen wuce gona da iri da kuma aiwatar da manufar kisan kai da ta'addanci kan al'ummar Palastinu.
Sakamakon wadannan munanan ayyuka da suka saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta mutane 97 ne suka yi shahada a kuma jikkatar Falasdinawa sama da 230 da ke zaune a zirin Gaza.
Your Comment